Kamfanin Dillancin Labarai Na AhlulBaiti

Madogara : Hausatv
Laraba

16 Maris 2022

19:29:59
1239953

Rasha Ta Kakabawa Manyan Jami’an Amurka Takunkumi

Gwamnatin Moscow ta kakaba takunkumi kan shugaban Amurka Joe Biden, da sakataren harkokin wajen Amurkar Antony Blinken, sakataren tsaro Lloyd Austin da wasu manyan jami'ai da dama, tare da haramta musu shiga Rasha a matsayin mayar da martani.

Kamfanin dillancin labarai na Ahlul-Baiti {a.s} - ABNA - Ma'aikatar harkokin wajen Rasha ta sanar cewa wannan na, a matsayin martani ga takunkumin da Amurka ta kakabawa Rasha da manyan jami'anta saboda rikicin Ukraine.

Rasha ta kuma yi gargadin cewa nan ba da jimawa ba Moscow za ta ba da sanarwar karin takunkumi kan wasu jami'an Amurka da suka hada da jami'an soja, 'yan majalisa, 'yan kasuwa, da kuma kafofin yada labarai.

Amma Rachar ta ce kofa a bude take don tuntubar juna.

Amurka dai ta sanya wa Rasha da manyan jami’anta takunkumi ne game da yakin Ukraine, inda ta haramtawa shugaban Rasha Vladimir Putin da ministan harkokin wajen kasar Sergei Lavrov shiga Amurka.

Amurka da kawayenta na Turai sun kuma kakaba wa Rasha takunkumin tattalin arziki.

342/