Kamfanin Dillancin Labarai Na AhlulBaiti

Madogara : Hausatv
Talata

15 Maris 2022

20:00:56
1239619

Jamus Ta Bayyana Cewa: Katse Sayen Makamashi Daga Rasha Zai Jefa Al’ummar Kasarta Cikin Talauci

Jaridar “ Guardian” ta Birtaniya ta ambato mahukuntan kasar Jamus suna cewa; Yanke amfani da makamashin kasar Rasha kai tsaye zai iya jefa kasar cikin taluaci.

Kamfanin dillancin labarai na Ahlul-Baiti {a.s} - ABNA - Ministan tattalin arzikin kasar Jamus Robert Habeck ya kara da cewa; Idan har kasarsa ta dakatar da sayen man fetur da iskar Gas daga jamus, to jamusawa za su fada cikin rashin lafiya, talauci da kuma kasa dumama gidajensu.

Robert ya kara da cewa; Kasashen kadan ne a cikin kasashen turai su ka dogar da makamashin kasar Rasha, kamar Jamus, domin daga can ne take samun kaso 55% na Gas, da kaso 52 % na gawayin coal da kuma nau’oi na mai ake amfani da su a Jamus, da sun kai kaso 34%.

Ministan tattalin arzikin kasar na Jamus ya kuma ce kasar tasa za ta yi kokarin rage dogaro da makamashin kasar Rasha, amma sannu a hankali ba lokaci daya ba, domin zai jefa kasar tasa cikin hatsari.

342/