Kamfanin dillancin labarai na Ahlul-Baiti {a.s} - ABNA - Wakilin na kasar Rasha a MDD ya cigaba da cewa; Da akwai jerin dakunan bincike 30 akan makamai masu guba a fadin kasar Ukiraniya, da su ka kunshi yadda za a samar da cutuka masu hatsari, tare da yin gargadin cewa za su iya fadawa a hannun ‘yan ta’adda.
A jiya Juma’a ne dai kwamitin tsaro na MDD ya yi zama na musamman bisa bukatar Rasha, domin a tattauna yadda Amurka ta taimakawa Ukiraniya wajen kafa dakunan bincike na samar da cutuka masu hatsari da suka hada da kwalara da wasu cutuka.
Jakadan na kasar Rasha a MDD ya kuma ce; Amurkan tana son yin amfani da tsuntsayen jemage wajen yada cutukan akan iyakar kasar Rasha.
Tun da fari, kasar Rasha ta sanar da kama dakunan bincike na kimiyya masu yawa a cikin kasar Ukiraniya wadanda ta ce Amurkan tana amfani da su wajen samar da cutuka.
342/