Kamfanin Dillancin Labarai Na AhlulBaiti

Madogara : Hausatv
Asabar

5 Maris 2022

20:38:29
1236245

Erdogan Ya Yi Tayin Karbar Tattaunawa Tsakanin Rasha Da Ukraine

Shugaban kasar Turkiyya ya yi tayin karbar bakuncin tattaunawa tsakanin Rasha da Ukraine.

Kamfanin dillancin labarai na Ahlul-Baiti {a.s} - ABNA - Recep Tayyip Erdogan ya nanata aniyarsa ta tattaunawa "a matakin shugabannin" na kasashen biyu tare da bayyana aniyarsa ta kiran Vladimir Putin a ranar Lahadi domin tsaida yaki.

Dama kafin hakan a ranar Juma'a, ministan harkokin wajen Turkiyya ya bayyana fatan samun damar haduwa da takwarorinsa na Rasha da na Ukraine a taron diflomasiyya da aka shirya yi tsakanin ranakun 11 zuwa 13 ga Maris din nan a birnin Antalya, da ke gabar teku a kudancin Turkiyya.

Turkiyya dai memba ce ta kungiyar NATO kuma ta kasance da Rasha a wasu fagage.

342/