Kamfanin Dillancin Labarai Na AhlulBaiti

Madogara : Hausatv
Jummaʼa

4 Maris 2022

20:43:33
1235905

Ukrain: Sojojin Rasha Suna Kusa Da Fadar Shugaban Kasar Ukrain A Birnin Kiev

A dai dai lokacinda sojojin Rasha suke kara nosawa cikin biranen kasar Ukrain, tashar talabijin ta Almayadeen ta kasar Lebanon ta bada labarin cewa sojojin Rasha a Kiev babban birnin kasar, suna kilomita kimani 24 kacal daga fadar shugaban kasar ta Ukrain.

Kamfanin dillancin labarai na Ahlul-Baiti {a.s} - ABNA - Har’ila yau wasu labarai sun bayyana cewa wuta ta tashi a cibiyar makamashin nukliyar ta kasar Ukrai a jiya sanadiyyar barin wutan da sojojin Rasha suka yi a kanta.

Labarin ya kara da cewa sojojin Rasha suna kara nosawa zuwa manya-manyan biranen a kasar Ukrai, wadanda suka hada da Energodar, da kuma wasu birane a jihohi daban-daban na kasar.

Har’ila yau a wani labarin kuma wani babban kwamnadan sojojin kasar Rasha Manjo Janar Andrey Sukhovetsky ya rasa ransa a cikin yakin na Ukrain, bayan da wani daga cikin masu harbi da bindiga daga nesa ya gano shi ya kuma kashe shi.

Sukhovetsky, dan shekara 41 a duniya shi ne mataimkin kwamandan bataliya na 41 na sojojin Rasha, sannan ya rike mukamai da dama a cikin sojojin kasar Rasha.

342/