Kamfanin Dillancin Labarai Na AhlulBaiti

Madogara : Hausatv
Jummaʼa

4 Maris 2022

20:39:56
1235904

Gwamnatin Rasha Ta Dakatar Da Watsa Shirye-Shiryen Wasu Kafafen Yada Labarai Na Kasashen Yamma

Gwamnatin kasar Rasha ta bada sanarwar dakatar da watsa shirye-shiryen wasu kafafen yana labarai na kasashen yamma da harshen Rashanci.

Kamfanin dillancin labarai na Ahlul-Baiti {a.s} - ABNA - bayyana cewa kafafen yada labarai wadanda abin ya shafa dai sun hada da BBC-Rasha da Libaty Radiyo Da Kuma Meduza Media.

Hukumar da ke kula da harkokin watsa labarai a ma’aikatar sadarawa ta kasar Rasha ta bayyana cewa ta tsaida wadannan kafafen yada labarai ne saboda labaran kariya da suke yadawa dangane da yakin da ke faruwa a kasar Ukrain.

Amma kasashen yamma suna zargin cewa gwamnatin shugaba Putin ta sake maida dokokin takaita ayyukan kafafafen yada labarai a kasar Rasha zuwa kamar yadda suke a tsohuwar tarayyar Soviet.

Kasar Rasha ba ta amfani da Kalmar ‘mamayar kasar Ukrain' a yakin da take fafatawa a kasar, amma kasashen yamma suna amfani da wadannan kalmomi da kuma wadanda suka fisu muni a kakafen yada labaransu.

Shugaban Putin dai ya bayyana cewa yakin kasar Ukrain, yaki ne na musamman ba mamayan kasar ba. Yaki ne na hana Ukrain mallakan makaman nukliya da kuma hanata shiga kungiyar tsaro ta NATO.

342/