Kamfanin Dillancin Labarai Na AhlulBaiti

Madogara : Hausatv
Alhamis

3 Maris 2022

17:35:28
1235588

Rasha Da Ukraine Sun Shiga Zagaye Na Biyu Na Tattaunawa

Kasashen Rasha da Ukraine sun shiga zagaye na biyu na tattauna a wannan Alhamis, a daidai lokacin da aka shiga kwana na takwas na matakin sojin da kasar Rasha ta ce tana dauka kan Ukraine.

Kamfanin dillancin labarai na Ahlul-Baiti {a.s} - ABNA - Mataimaki ga shugaban kasar Rasha, kuma jagoran tawagar kasar a tattaunawa da Ukraine Vladimir Medinsky, ya ce tawagar da yake shugabanta ta isa Belovezhskaya Pushcha, dake kan iyakar Belarus da Poland, domin shiga tattaunawa karo na biyu da wakilan Ukraine.

Mr. Medinsky ya ce, akwai tsammanin za a tattaunawa game da yiwuwar tsagaita bude wuta yayin zaman na biyu, tare da sauran muhimman batutuwa.

Kafin hakan dai babban zauren Majalisar Dinkin Duniya ya kada kuri'a da gagarumin rinjaye na neman Rasha ta janye daga kutsen da ta kaddamar a kan Ukraine, wajen tsaida fada da janye dakarunta.

Yayin kada kuri'ar kasashe mambobi 141 daga cikin 193 suka amince da wannan kudiri na MDD lokacin zaman babban zaurenta na ba kasafai ba.

342/