Kamfanin Dillancin Labarai Na AhlulBaiti

Madogara : Hausatv
Alhamis

3 Maris 2022

17:34:05
1235586

WHO : Rikicin Rasha Da Ukraine Zai Kara Yada Annobar Korona

Hukumar Lafiya ta Duniya (WHO) ta yi gargadin cewa rikicin Rasha da Ukraine na iya haifar da yaduwar COVID-19 kuma hakan yana kara barazanar kamuwa da cutar mai yawa.

Kamfanin dillancin labarai na Ahlul-Baiti {a.s} - ABNA - Ya kamata gwamnatoci su sake yin la'akari da matakan yaki da annobar tare da hanzarta shirye-shiryen rigakafi don rage yaduwar nau’in Omicron, in ji babban darektan WHO.

"WHO ta damu matuka game da tabarbarewar ayyukan jin kai a Ukraine," in ji Darakta Janar na WHO Tedros Adhanom Ghebreyesu a wani taron manema labarai.

"Kafin rikicin, Ukraine ta sami karuwar adadin masu kamuwa da COVID-19 a baya-bayan nan.

Hukumar kula da 'yan gudun hijira ta Majalisar Dinkin Duniya, ta ce kimanin, mutane miliyan ne suka bar Ukraine, kuma ana sa ran adadin zai karu cikin sauri, wanda hakan zai iya haifar da yaduwar annobar tsakanin jama’a.

342/