Kamfanin Dillancin Labarai Na AhlulBaiti

Madogara : Hausatv
Alhamis

3 Maris 2022

17:28:16
1235579

​Rasha Ta Ce Ta Na Iko Da Birnin Kherson A Rana Ta 7 Da Fara Yaki A Ukrain

Gwamnatin kasar Rasha ta bada sanarwan cewa ta karbi iko da birnin Kherson dake kudancin kasar Ukrain.

Kamfanin dillancin labarai na Ahlul-Baiti {a.s} - ABNA - Tashar talabijin ta Presstv a nan Tehran ta nakalto kakakin ma’aiakatar tsaron kasar Rasha yana fadar haka a jiya Talata. Ya kuma kara da cewa birnin Kherson yana bakin tekun Black Sea ne, kuma yana da yawan mutane kimani 250,000.

Magajin garin birnin Igor Kolykhayev ya bayyana cewa sojojin Rasha sun kwace tashar jiragen ruwa na birnin da kuma tashar jiragen kasa a daren jiya Talata. Kuma yana ganin nan da wani lokaci sojojin zasu mamaye larding aba daya.

A wani labarin kuma majiyar gwamnatin kasar Ukrain ta bada sanarwan cewa sojojin Rasha masu sauka da lema sun dira a cikin birnin na biyu mafi girma a kasar wato Kharkiv, wanda hakan ya jawo tserewar mutanen daga kan tutinu, da kuma yaki tsakanin sojojin na Rasha da kuma na Ukrain da suke cikin Birnin.

Anton Gerashchenko, mai bawa ministan cikin gida na kasar Ukrain ya bayyana a cikin shafinsa na Telegram kan cewa fada ya barke a wata makarantar sojoji a birnin, kuma ya zuwa yanzu kusan babu wani wuri wanda makaman igwa basu tab aba a cikin birnin.

342/