Kamfanin Dillancin Labarai Na AhlulBaiti

Madogara : Hausatv
Laraba

2 Maris 2022

17:30:44
1235207

Shugaban Kasar Amurka Ya Ce; Kasarsa Ba Za Ta Shiga Yaki Da Kasar Rasha Ba

Shugaban na kasar Amurka Joe Biden wanda ya gabatar da jawabi a zaman hadin gwiwa na shekara-shekara da majalisun dokoki da dattawa ke yi, ya ce; Babu yadda za a yi kasarsa ta shiga cikin yaki da kasar Rasha,amma dai za ta yi kokarin hana Rasha yin kutse cikin wasu kasashen na turai.

Kamfanin dillancin labarai na Ahlul-Baiti {a.s} - ABNA - Shugaban kasar ta Amurka ya kara da cewa; Amurka za ta kare kowane taku na kasashen da suke mambobi a kungiyar yarjejeniyar tsaro ta Nato.

Shugaban kasar ta Amurka ya kuma ce; Amurka da kawayenta sun kakabawa Rasha takunkumi mai tsanani da zai hana ta samun kere-kere na zamani.

342/