Kamfanin Dillancin Labarai Na AhlulBaiti

Madogara : Hausatv
Laraba

2 Maris 2022

17:29:12
1235205

Rasha Ta Ce Za Ta Ci Gaba Da Kai Hari A Ukraine Har Sai Ta Cimma Burinta

Ministan tsaron kasar Rasha Sergei Shoigu ya bayyana cewa, kasarsa za ta ci gaba da kaddamar da aikin soji na musamman a kasar Ukraine, har sai kasar ta cimma babbar manufar kare kanta daga barazanar da kasashen yamma ke yi mata.

Kamfanin dillancin labarai na Ahlul-Baiti {a.s} - ABNA - M. Shoigu ya fada a yayin wani taro da manyan jami’an tsaron kasar suka gudanar ta kafar bidiyo cewa, abu mai muhimmanci a gare mu shi ne, kare kasar Rasha daga barazanar soji daga kasashen yammacin duniya, wadanda ke kokarin yin amfani da al'ummar Ukraine wajen yakar kasarmu. Ya kara da cewa, sojojin Rasha ba sa mamaye yankin Ukraine, kuma suna daukar dukkan matakan kare rayuka da lafiyar fararen hula. Shoigu ya ce, ina son in jaddada cewa, ana kai hare-haren ne kawai a kan wuraren da sojoji suke da kuma makamai na musamman.

Yau dai an shiga kwana na bakwai na matakin sojin da Rasha ta ce tana dauka kan Ukraine domin kakkabe ta daga wadanda ta danganta da ‘yan nazi. Ministan harkokin wajen kasar Rasha Sergei Lavrov ya bayyana kasancewar makamman nukiliyar Amurka a yankin a matsayin abin da Moscow ba za ta amince da shi ba, yana mai gargadin cewa Rasha ba za ta yi kasa a gwiwa ba wajen hana Ukraine samun irin wadannan muggan makamai, Hasali ma hakan ya saba wa yarjejeniyar hana yaduwar makaman nukiliya (NPT), inji shi. A jiya shugaban Amurka Joe Biden ya bayyana cewa kasarsa za ta bi sahun kasashen turai da kuma Canada domin haramtawa jiragen saman Rasha keta hazonta.

342/