Kamfanin Dillancin Labarai Na AhlulBaiti

Madogara : Hausatv
Litinin

28 Faburairu 2022

20:15:48
1234531

An Kammala Tattaunawa Tsakanin Tawagogin Rasha Da Ukraine A Kasar Belerus

An kammala zagaye na farko na tattaunawa tsakanin tawagogin kasashen Rasha ta Ukraine a kasar Belerus a cikin ‘yan sa’o’in da suka gabata.

Kamfanin dillancin labarai na Ahlul-Baiti {a.s} - ABNA - Tashar talabijin ta Daya, ta kasar Rasha ta bada labarin cewa taron neman tsagaiuta budewa juna wuta yak are ba tare da an san sakamakon taron ba. Dukkan bangarorin biyu basu yi wani bayani dangane da tattaunwarba.

Tawagar kasar Ukraine mutanen 5 ne wanda mataimkin ministan harkokin wajen kasar ya Jagoranta. A bangaren Rash kuma tawagar ta hana da kwararru, da jami’an ma’aikatar harkokin waje da na ma’aikatar harkokin tsaronm kasar.

Labarin ya kara da cewa tuni tawagr Ukraine ta bar kasar Belerus zuwa gida. A ranar Alhamis da ta gabata ce shugaban kasar Rasha Vladimir Putin ya bada umurni ga sojojin sa su shiga kasar Ukrain don kare yankunan da kabilun rasha suke zama wanda ake kira Donbas.

A yau ne yakin ya shiga kwana na biyar da farashi. Kasashen yamma tuni sun kakabawa kasar Rasha takunkuman tattalin arziki masu tsanani na, bankuna da kasuwanci da sauransu.

342/