Kamfanin Dillancin Labarai Na AhlulBaiti

Madogara : Hausatv
Litinin

28 Faburairu 2022

20:07:17
1234523

​Yakin Ukraine: Ana Nunawa ‘Yan Afirka Bakaken Fata Banbanci A Ukraine Bayan An Fara Yaki

Gwamnatin Najeriya ta nuna takaicinta da labaran da suke isa daga kasar Ukrain na cews ana muzgunawa yan kasar wadanda suke kokarinsu shiga kasar Poland saboda tsira da ransu daga yankin da aka fara a kasar.

Kamfanin dillancin labarai na Ahlul-Baiti {a.s} - ABNA - Shafin yanar gizo na Labarai ‘Africanews’ ya nakalto Garba Shehu kakakin fadar shugaban kasa a Abuja yana fadar haka a yau Litinin. Ya kuma kara da cewa ‘Akwai wasu labaran da suke isa kunnuwammu kan cewa jami’an tsaron kasar Ukrain suna hana ‘yan Najeriya shiga Motocin Bus Bus da da kuma jiragen kasa don shiga kasar Poland.

Labarin ya kara da cewa akwai ‘yan Najeriya kimani 4000 a kasar Ukrain, mafi yawansu daliban jami’o’ii ne. Kamar Sauran Mutane su ma suna kokarin ganin sun shiga kasar Poland don tsira da ransa daga yakin da aka fara a kasar.

Amma jakadan Najeriya a kasar Ukrain Mr Joanna Tarnawska ya tabbatarwa wasu kafafen yada labarai kan cewa yana kula da yadda al-amura suke tafiya a kan iyakar kasar Poland da Ukrain, kuma a halin yanzu wasu yan Najeriya sun shiga kasar ta Poland.

342/