Kamfanin Dillancin Labarai Na AhlulBaiti

Madogara : Hausatv
Litinin

28 Faburairu 2022

20:06:02
1234522

Rasha Ta Sanar Da Cewa Jiragen Samanta Na Yaki Ne Suke Da Iko Da Sararin Samaniyar Kasar Ukiraniya

Wannan sanarwar ta sojojin kasar Rasha ta zo ne dai adaidai lokacin da yaki da kasar Ukiraniya ya shiga cikin kwanaki na biyar da farawa.

Kamfanin dillancin labarai na Ahlul-Baiti {a.s} - ABNA - Rashan ta sanar da haka ne ,tana mai zargin kasashen yamma da nuna mata kiyayya.

A gefe data ma’aikatar harkokin wajen kasar Blarus ta sanar da cewa; An kammala duk wasu shirye-shirye da suka dace domin karbar bakuncin tattaunawa a tsakanin tawagogin kasashe Rasha da kuma Ukiraniya.

Majiyar ta kara da cewa; A halin yanzu ana jiran isowar tawagogin kasashen biyu ne domin bude tattaunawa.

Sai dai majiyar watsa labaru ta kasar Rasha Sputnik ta ce; Tuni tawagar kasar Ukiraniya ta isa cikin kasar Blaruss. Ana kuma sa ran cewa a yau Litinin ne za a bude tattaunawar tsakanin banagarorin biyu.

Kwanaki biyu bayan fara yakin ne dai kasar Rasha ta bukaci Ukiraniya da ta zauna da ita akan teburin tattaunawa domin warware matsalolin da su ka jawo rikicin.

342/