Kamfanin Dillancin Labarai Na AhlulBaiti

Madogara : Hausatv
Lahadi

27 Faburairu 2022

15:06:51
1234130

Rasha Ta Ce A Shirye Ta Ke Ta Tattauna Da Ukraine

Fadar gwamnatin Rasha ta Kremlin ta ce a shirye ta ke ta hau teburun tattauna da Ukraine a binrin Gomel na Bielorus.

Kamfanin dillancin labarai na Ahlul-Baiti {a.s} - ABNA - Rasha ta ce tawagarta ta ma’aikatar harkokin waje da ta tsaro da kuma wasu ma’aikattu ciki har da na fadar shugaban kasa sun isa Belarus domin tattaunawa da Ukraine.

Saidai shugaban Ukraine Volodymyr Zelensky, ya ce kasar za ta shiga tattaunawar amma ba a Bielorus ba.

A wani lokaci yau Lahadi ne ake sa ran kwamitin tsaron MDD, zai sake yin wani zama game da rikicin na Rasha da Ukraine.

342/