Kamfanin Dillancin Labarai Na AhlulBaiti

Madogara : Hausatv
Lahadi

27 Faburairu 2022

14:59:23
1234121

Yakin ​Ukraine: Ana Barin Wuta A Birnin Kiev Tsakanin Sojojin Rasha Da Ukraine

Ana fafatawa tsakanin sojojin Rasha da na Ukrain a birnin Kiev babban birnin kasar Ukrain, a dai-da lokacinda aka shiga kwanaki 3 da sojojin Rasha suka shiga kasar Ukrai da sunan kare yankunan Ukrain biyu da suka balle daga kasar.

Kamfanin dillancin labarai na Ahlul-Baiti {a.s} - ABNA - Tashar talabijin ta Presstv a nan Tehran ta bayyana cewa gwamnatin Amurka ta yi tayin fitar da shugaban kasar Ukrain Volodymyr Zelensky daga kasar idan ya amince.

A birnin Paris kuma shugaba Emmanuel Macron ya ce yaki a Ukrain zai yi tsawo har’ila yau duk wani rikicinda ya tashi sanadiyyar yakin, shi ma zai yi tsawo kamar yakin. Shugaban ya bayyana haka ne a wata kasuwar baje koli ta kayakin gona a birnin Paris.

Har’ila yau kakakin fadar shugaban kasar Ukrain ya ce, jami’an gwamnatin kasar Rasha da na Ukrai zasu gana a cikin sa’o’i masu zuwa don tattauna batun tsagaita bude wuta. Ya zuwa yanzu dai mutane 198 ne aka tabbatar da mutuwarsu tun bayan fara yakin a ranar Alhamis da ta gabata.

342/