Kamfanin Dillancin Labarai Na AhlulBaiti

Madogara : Hausatv
Asabar

26 Faburairu 2022

13:57:42
1233735

MDD : Rasha Ta Ki Amincewa Da Kudurin Kin Matakin Sojin Da Ta Dauka Kan Ukraine

Kasar Rasha ta ki amincewa da kada kuri'a a kwamitin sulhu na Majalisar Dinkin Duniya, da aka gabatar na nuna rashin amincewarsu da matakin sojin da ta dauka kan Ukraine, da kuma gaggauta janye dakarunta daga Ukraine din.

Kamfanin dillancin labarai na Ahlul-Baiti {a.s} - ABNA - Amurka da Albaniya ne suka gabatar kudurin wanda kuma ke bukatar Rashar ta gaggauta janye dakarunta daga Ukraine din.

Daga cikin mambobin kwamitin guda 15, kasashe 11 ne suka kada kuri'ar amincewa da kudurin, yayin da uku suka kaurace wa kuri'ar da suka hada da China, Indiya da Hadaddiyar Daular Larabawa.

342/