Kamfanin Dillancin Labarai Na AhlulBaiti

Madogara : Hausatv
Asabar

26 Faburairu 2022

13:56:58
1233734

Najeriya : Buhari Ya Saka Hannu Kan Sabuwar Dokar Zabe

Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya sanya hannu kan sabuwar dokar zabe ta kasar wadda aka dauki tsawon lokaci ana ka-ce-na-ce a kai.

Kamfanin dillancin labarai na Ahlul-Baiti {a.s} - ABNA - Buhari ya saka hannu kan dokar ne ranar Juma'a, a fadarsa.

Da yake jawabi lokacin da yake sanya hannu kan dokar, shugaban ya bukaci 'yan majalisar da su hanzarta yin gyara ga sashe na 84 na dokar wanda ya tanadi haramta wa masu rike da mukaman gwamnati jefa kuri'a a zaben shugabannin jam'iyya ko kuma na 'yan takara.

Shugaban ya ce wannan sabuwar dokar zaben, za ta kara inganta harkar zabe.

Da yake jawabi yayin zaman saka wa dokar hannu, Shugaba Buharin ya ce kudurin dokar na yanzu da aka yi wa gyara ya fi inganci sosai da wanda aka fara kawo masa.

342/