Kamfanin Dillancin Labarai Na AhlulBaiti

Madogara : Hausatv
Asabar

26 Faburairu 2022

13:55:21
1233732

Zelensky : An Kyale Ukraine Ita Kadai Ta Yaki Rasha

Shugaban kasar Ukraine Volodymyr Zelensky, ya bayyana cewa, an kyale kasarsa ita kadai ta yaki Rasha, bayan da Fadar Kremlin ta sanar da daukar matakan soji kanta.

Kamfanin dillancin labarai na Ahlul-Baiti {a.s} - ABNA - Ya kuma kara da cewa, ba ya tsoron hawan teburin sulhu da Rasha.

Shi ma dai shugaba Putin na Rashar ya ce a shirye ya ke ya tura tawagar gwamnatinsa zuwa Minsk, domin shiga tattaunawar da za a yi tare da tawagar kasar Ukraine.

342/