Kamfanin Dillancin Labarai Na AhlulBaiti

Madogara : Hausatv
Jummaʼa

25 Faburairu 2022

20:13:21
1233417

Rahotanni daga kasar Ukiraniya sun ambaci cewa sojojin Rasha sun fara kutsawa cikin babban birnin kasar Kiev

Tashar talabijin din Aljazeera ta ambaci cewa; Ana yin bata-kashi mai tsanani a tsakanin sojojin kasar Rasha da sojojin Ukiraniya a cikin unguwar Abolon da take cikin birnin Kiev.

Kamfanin dillancin labarai na Ahlul-Baiti {a.s} - ABNA - Tun a jiya Alhamis ne dai sojojin kasar Rasha su ka shelanta yaki akan kasar Ukiraniya ta bangarori daban-daban da su ka hada da Danbass da Lungas da suke kan iyaka. Yankunan biyu dai sun sanar da ballewa daga kasar Ukiraniya inda su ka shelanta kawukwansu a matsayin masu cin gashin kai.

Rasha ta amince da ‘yancin yankunan, inda ta kulla yarjejeniyar tsaro da su, da hakan ya ba ta damar aikewa da sojojin domin kare su daga hare-haren sojojin Ukiraniya.

342/