Kamfanin Dillancin Labarai Na AhlulBaiti

Madogara : Hausatv
Jummaʼa

25 Faburairu 2022

20:05:04
1233412

Kasashen Yammacin Duniya Na Mayar Da Martani Kan Matakin Sojin Rasha Kan Ukraine

Manyan kasashen yammacion duniya na ci gaba da mnayar da martani kan matakin sojin da Rasha ta dauka kan Ukraine.

Kamfanin dillancin labarai na Ahlul-Baiti {a.s} - ABNA - Shugaban Amurka Joe Biden ya sanar da cewa kawayen Amurka za su kakaba wa Rasha takunkumai masu tsanani.

Shugaban Faransa Emmanuel Macron ya ce wannan wani lokaci ne da aka samu sauyin al'amura a tarihin Turai.

Firaministan Birtaniya Boris Johnson ya ce Mr Putin ya zabi bin hanyar zubar da jinni.

Kasashen faransa da kuma Biritaniya sun bukaci taron kungiyar tsaro ta NATO cikin lokaci mafi sauki.

China ta ce ta na fahimtar damuwar da Rasha ta ke da ita game da batun tsaronta.

Tsohon shugaba Amurka Donald Trump ya ce shugaba Putun ya yi amfani ne da kasawa da kuma sakacin gwamnati mai ci.

A cikin daren jiya ne Shugaban kasar Rasha Vladimir Putin ya yi jawabi ta kafar telabijin, inda ya sanar da yanke shawarar kaddamar da wani matakin soja na musamman a yankin Donbass.

Kana shugaban ya ce kasar Rasha ba ta da shirin mamaye kasar Ukraine.

342/