Kamfanin dillancin labarai na Ahlul-Baiti {a.s} - ABNA - Shugaban Ukraine din Volodymyr Zelensky ne ya bayyana hakan a yayin wani jawabi ga manema labarai.
M. Zelensky, ya kuma zartas da dokar ta-baci mai wa’adin kwanaki 30 a daukacin yankunan kasar, ban da jihohin Donetsk da Luhansk.
dokar ta fara aiki ne daga yau, 24 ga wata.
Dokar da ta fara aiki a ranar Alhamis, ta hana gudanar da gangami, da zanga-zanga, da yajin aiki, da sauran ayyukan da za su haddasa taruwar jama’a.
Kana an haramtawa sojoji sauya wuraren zamansu, da tsaurara manufar da ta shafi shige da fice.
A 'yan awannin da suka wuce magajin garin Kyiv babban birnin kasar ya sanar da kafa dokar hana fitar dare a fadin birnin, Wacce za ta fara aiki daga tsakanin karfe 10 na dare zuwa 7 na safe a kullum.
342/