Kamfanin dillancin labarai na Ahlul-Baiti {a.s} - ABNA - A jiya laraba ce ministan harkokin wajen kasar Ukrain Dmytro Kuleba ya bukacin kwamitin tsaro na majalisar dinkin duniya day a kira zaman gaggawa saboda bukatar da yankunan Donetsk da Luhansk suka mikawa mahukumtan rasha na aikewa da sojoji saboda yadda yanayin tsaro yake kara tabarbarewa a wajen
An kara samun takun saka ne bayan da Amurka ta zargi kasar Rasha da aikewa da sojojinta 15,000 a kusa da iyakar kasar, domin kai mata hari da mamayeta, kuma an zargi Amurka da kawayenta da nuna damuwa kan lamarin.
342/