Kamfanin Dillancin Labarai Na AhlulBaiti

Madogara : Hausatv
Laraba

23 Faburairu 2022

13:53:11
1232718

Kungiyar tarayyar Turai Ta Kakabawa Kasar Rasha Sabbin Takunkumi

Ministan harkokin wajen kungiyar tarayyar Turai ya gudanar da taron gaggawa don amincewa da kakabawa yan majalisar dokokin Rasha guda 351 takunkumi wanda suka kada kuri’ar amincewa da bawa yankuna biyu dake gabashin kasar Ukrain Yancin cin gashin kai,

Kamfanin dillancin labarai na Ahlul-Baiti {a.s} - ABNA - Kasahen na turai sun ce wannan somi tabi ne da sannu za su shigar da bangaren kasuwanci da kudade da kafafen sadarwa cikin takunmi kuma a dakatar da su daga kungiyar

Daga cikin takunkumin ya kunshi rike dukkan kadarorin kasar da kuma hana tafiye tafiye, shirin shinfida bututun iskar gasa daga kasar rasha zuwa kasar Jamus kusan an kusa rufewa , wannan yana zuwa ne duk da tsananin bukatar da kungiyar Eu ke da shi na makamashi kasar Rasha,

Yanzu haka dai kungiyar na duba yiyuwar bin wata hanyar samar da iskar gasa don ta rage dogaro da kasar rasha, tana tuntubar kasashen Japan koriya ta kudu Qatar Azarbaijan da kasar masar sai dai hanya ce mai tsada don sai an yi safarashi ta jirgin ruwa , amma gas din rasha yafi arha sosai kuma tuni dama akwai bututun da aka shinfida domin aikewa da iskar gas din.

342/