Kamfanin Dillancin Labarai Na AhlulBaiti

Madogara : Hausatv
Laraba

23 Faburairu 2022

13:51:02
1232717

Kasashen EU Sun Amince Da Shirin Kakabawa Rasha Takunkuman Tattalin Arziki

Jami’i mai kula da al’amuran harkokin waje na kungiyar tarayyar Turai Josept Borrel ya bayyana cewa kasashen kungiyar gaba daya sun amince da shirin kakabawa kasar Rasha takunkuman tattalin arziki a jiya da yamma.

Kamfanin dillancin labarai na Ahlul-Baiti {a.s} - ABNA - Majiyar muryar Jumhuriyar Musulunci ta Iran ta bayyana cewa yankin Dombos da ke gabacin kasar Ukrain wanda ya hada Dontesk da Luhansak da kuma wasu yankunan a gabancin kasar Ukrain sun shelanta bellewarsu daga kasar Ukrain a shekara ta 2014 bayan da aka yi sauyin shugabanci a kasar.

A daren Litinin da ta gabata ce shugaban kasar Rasha Vladimir Putin ya amince da samun ‘yencin yankunan Donstek da kuma Lohansek wadanda mafi yawan ma zaunansu yan kabilar Rashe ne, ya amince su zama ‘yentattun kasashe.

Kimani watanni biyu da suka gabata ne shugaban kasar Amurka Joe Biden ya fara yayata cewa kasar Rasha na kokarin mamaye kasar Ukrain.

Borrel ya bayyana cewa takunkuman da za’a dorawa kasar Rasha saboda shiga cikin harkokin kasar Ukrain a matsayin ‘yentacciyar kasa ne.

342/