Kamfanin Dillancin Labarai Na AhlulBaiti

Madogara : Hausatv
Talata

22 Faburairu 2022

15:43:51
1232361

​ Putin: Amurka Ce Kanwa Uwar Gami A Rikicin Kasar Ukiraniya

A wata ganawar da shugaban kasar Rasha ya yi da majalisar koli ta tsaron kasarsa sa’o’i kadan da suka gabata, Vladimir Putin ya bayyana cewa; Yin amfani da kasar Ukiraniya a matsayin kodagon dara da Amurka take yi wani abu ne mai hatsarin gaske.

Kamfanin dillancin labarai na Ahlul-Baiti {a.s} - ABNA - Shugaban na kasar Rasha ya kuma bayyana cewa; Nan da wani lokaci a yau zai yanke hukunci akan daukar yankunan Donetsk da Donbass na kasar Ukiraniya a matsayin kasashe masu cin gashin kansu.

Tun da fari, yankunan biyu sun yi kira ga gwamnatin kasar Rasha da ta amince da su a matsayin jamhuriyoyi masu zaman kansu. Su ma ‘yan majalisar koli ta tsaron kasar Rasha da suka hada da ministan tsaro Sergey Shoigu sun amince da yankunan biyu na Ukiraniya su zama jamhuriyoyi masu cin gashin kansu.

Rahotannin da suke fitowa daga Kasar Rasha sun ce, a yau Litinin an yi musayar wuta a tsakanin sojojin kasashen biyu akan iyakar kasar Rasha. Kafafen watsa labarum Rasha sun ce; wasu masu dauke da makamai sun yi kokarin ketara iyakarta, sai dai sojojinta sun halaka biyar daga cikinsu.

342/