Kamfanin Dillancin Labarai Na AhlulBaiti

Madogara : Hausatv
Talata

22 Faburairu 2022

15:42:54
1232360

Kamfanonin Jiragen Sama Da Dama Na Duniya Sun Dakatar Da Jigila Zuwa Kasar Ukiraniya

Kamfanonin jiragen sama na bayan nan da suka dakatar da zuwa birnin Kiev, su ne; “Air Farance” da “ KLM” na kasar Holland sai kuma kamfanin jiragen sama na kasa Jamus “ Lufthansa”.

Kamfanin dillancin labarai na Ahlul-Baiti {a.s} - ABNA - turai sun dauki wannan matakin ne a daidai lokacin da ake zaman dardar yake karuwa a kasar ta Ukiraniya saboda tsoron barkewar yaki da kasar Rasha.

Sai dai har ya zuwa yanzu Hukumar da take kula da zirga-zirgar jiragen sama ta kasa da kasa ba ta fitar da sanarwa hana zirga-zirga jiragen sama zuwa Ukiraniya ba.

Kasar Rasha dai ta girke sojojin sama da na ruwa da na kasa a zagaye da kasar ta Ukiraniya, inda ake jin tsoron cewa yaki zai iya barkewa a kowane lokaci daga yanzu.

Rasha dai tana zargin kasashen turai da Amurka da yi wa kasar Ukiraniya ingiza mai kantu ruwa, ta hanyar lasa mata zuba a baki na shigar da ita kungiyar yarjejeniyar tsaro ta Nato.

342/