Kamfanin Dillancin Labarai Na AhlulBaiti

Madogara : Hausatv
Litinin

21 Faburairu 2022

17:16:09
1232042

Ra’isi : Duk Wata Yarjejeniya A Vienna Dole Ne Ta Kunshi Dage Takunkumi

Shugaban kasar Iran, Ebrahim Ra’isi ya bayyana cewa dole ne duk wata yarjejeniya da za’a iya cimma a tattaunawra Vienna, ta kunshi dage takunkumi da kuma tabbaci a zahiri.

Kamfanin dillancin labarai na Ahlul-Baiti {a.s} - ABNA - Da yake magana da shugaban Faransa Emmanuel Macron a wayar tarho ranar Asabar, shugaban na Iran ya ce Jamhuriyar Musulunci ta gabatar da shawarwari masu ma'ana a yayin shawarwarin, kuma ta yi la'akari da shawarwarin da wasu bangarorin suka gabatar a shawarwarin, dangane da dacewarsu da muradun al'ummar Iran."

A daya bangare kuma, yayin da yake ishara da irin rawar da Iran take takawa wajen yaki da ta'addanci tare da Iraki da Siriya, Raisi ya ce: Idan ba don yakin da Iran take yi da ta'addanci ba, musamman ma kokarin Shahid Qassem Soleimani, da Daesh ta fara gudanar da ayyukanta a Turai a yau.

A nasa bangaren kuwa shugaban Faransa Emmanuel Macron ya ce an samu ci gaba mai kyau a tattaunawar da ake yi a Vienna kuma suna fatan za a kammala tattaunawar cikin gaggawa.

342/