Kamfanin Dillancin Labarai Na AhlulBaiti

Madogara : Hausatv
Litinin

21 Faburairu 2022

17:14:12
1232040

Sarauniya Elizabeth Ta Ingila Ta Kamu Da Cutar Korona

A sanarwar da fadar Buckingham ta fitar an bayyana cewa sarauniya na tattare da alamun sanyi amma ana sa ran za ta ci gaba da gudanar da ayyukanta sama-sama a mako mai zuwa.

Kamfanin dillancin labarai na Ahlul-Baiti {a.s} - ABNA - "Za a ci gaba da duba lafiyarta kuma za a bi duka hanyoyin da suka dace," kamar yadda fadar ta bayyana a sanarwa yau Lahadi.

Sarauniya Elizabeth mai shekara 95 ta hadu da babban danta kuma magajinta wato Yarima Charles wanda shi ma ya kamu da korona a makon da ya gabata.

342/