Kamfanin Dillancin Labarai Na AhlulBaiti

Madogara : Hausatv
Lahadi

20 Faburairu 2022

16:58:40
1231641

An Kulla Yarjejeniyar Aiki Tare A Tsakanin Kungiyoyin Tarayyar Turai Da Kuma Afirka A Birnin Brussels

Kungiyoyin biyu na nahiyoyin Afirka da Turai sun amince da cigaba da aiki tare a wata yarjejeniyar da suka kulla a jiya Juma’a a birnin Brussels cibiyar tarayyar Turai. Tarayyar ta turai ta amince da ta zaba hannun jari da ya kai Euro biliyan 150 a cikin muhimman cibiyoyi na nahiyar da kuma samar da allurer riga-kafin cutar Korona.

ABNA24 – Har ila yau kasashen turai din suna share fagen sassauta dokoki masu tsauri na bayar da Lamuni na Asusun IMF ga kasashen nahiyar ta Afirka.

Bayanin da shugaban kungiyar tarayyar Afirka Macky Sall ya fitar ya kunshi cewa; manufar taron wanda aka bude tun ranar Alhamis shi ne karfafa dankon alaka a tsakanin bangarorin biyu, saboda bunkasa harkokin zaman lafiya.

342/