Kamfanin Dillancin Labarai Na AhlulBaiti

Madogara : Parstoday
Asabar

19 Faburairu 2022

13:29:01
1231246

​Kungiyoyin Tarayyar Afrika da Ta Turai Suna Karfafa dangantakar dake tsakaninsu

Shugaban kungiayr tarayyar Afrika Musa Faki ya bayyana cewa AU da EU suna karfafa dangantaka a tsakaniunsu a taron da suke a kasar Beiljuim. Fakih ya bayyana hakan a wajen taron koli da ke gudana tsakani kungiyar Tarayyar turai da kuma takwararta ta Afrika wato AU a birnin Bruksel na kasar Belgium.

Taron ya hada shuwagabannin kasashen Afrika 40 daga kasashen a yunkurin EU na kara karfafa hulda tattalin arziki da sauran abokanta a fadin duniya a dai dai lokacin da kasahen Rash da china suke kara yin tasiri a nahiyar.

Daga cikin makasudin gudanar da taron na Koli akwai kokarin da kungiyar EU take yi na zuba hannun jari da yakai dalar Amurka biliyan 150 a nahiayr nan da shekaru 7 masu zuwa.

Anasa bangaren shugaban kasar Senegal Makky Sall yace har yanzu akwai sabanin sosai game da yadda za’a samar da kudaden ayyukan hako mai a nahiyar, kuma lamari ne mai matukar muhimmanci da ya kamata kungiyar EU ta yi la’akari da shi da kuma yadda za’a samar da kudaden da ake bukata don gudanar da wadannan ayyuka.

342/