Kamfanin Dillancin Labarai Na AhlulBaiti

Madogara : Hausatv
Jummaʼa

18 Faburairu 2022

18:22:33
1230920

Australia Za Ta Saka Hamas A Jerin Kungiyoyin 'Yan Ta'adda

Ostiraliya ta sanar cewa, za ta saka gabadayen kungiyar gwagwarmayar Islama ta Falasdinawa wato Hamas a jerin kungiyoyin da take wa kallon na ta'addanci.

Kamfanin dillancin labarai na Ahlul-Baiti {a.s} - ABNA - sakatariyar harkokin cikin gida ta kasar ta ce "manufofin Hamas da kungiyoyin masu tsattsauran ra'ayi ba su da wurin zama a Ostiraliya.

Ta kara da cewa yana da mahimmanci dokokinmu su maida hankali kan ayyukan ta’addanci da kuma ‘yan ta’addan, amma kuma yana da kyau mu hada har da wadanda ke shiryawa da tallafawa da aikata ayyukan ta’addancin.

Kungiyar Hamas da ke iko da zirin Gaza ta na gwagwarmya ne domin ‘yantar da Kudus, kuma ta sha shiga yaki da Isra’ila.

342/