Kamfanin Dillancin Labarai Na AhlulBaiti

Madogara : Hausatv
Laraba

16 Faburairu 2022

19:37:50
1230302

Kasashen Yamma Da Amurka Sun Yaba Da Matakin Rasha Na Janye Sojinta A Iyaka Da Ukraine

Kasashen Yamma Da Amurka Sun Yaba Da Matkin Rasha Na Janye Wani Bangaren Sojinta A Iyaka Da Ukraine, Amma Sun Ce Zasu Zura Ido Su ga gani in hakan ta wakana a zahiri.

Kamfanin dillancin labarai na Ahlul-Baiti {a.s} - ABNA - Shugaba Joe Biden na Amurka ya bayyana a wani gajeren jawabi cewa matakin wata alama ce mai kyau, amma bamu kai ga tabbatar da hakan ba kawo yanzu.

Shugaban na Amurka dai ya kiyasce cewa sojojin da Rasha ta jibge a iyaka da Ukraine sun haura dubu 150.

Kafin hakan Shugaban Rasha Vladimir Putin da shugaban gwamnatin kasar Jamus Olaf Scholz dake ziyara a Rasha, sun jadadda bukatar kaucewa shiga yaki kan batun Ukraine, tare da warware rikicin ta hanyar diflomasiyya.

Yayin wani taron manema labarai tare da Mr. Scholz, shugaba Putin ya ce, su ma ba sa son shiga yaki, shi ya sa ma suka gabatar da shawarar yadda za a yi sulhu, a kokarin cimma yarjejeniyar da za ta tabbatar da tsaro ga kowa.

A nasa bangaren, Alof Scholz ya ce, nahiyar Turai na fuskantar rikici mafi hadari da ba a gani ba cikin gomman shekaru, kuma akwai bukatar yayyafawa batun na Ukraine ruwan sanyi, domin kaucewa aukuwar yaki.

342/