Kamfanin Dillancin Labarai Na AhlulBaiti

Madogara : Hausatv
Laraba

16 Faburairu 2022

19:35:05
1230298

UAE Da Turkiyya Sun Rattaba Hannu Kan Yarjejeniyoyi Da Dama

Hadaddiyar Daular Larabawa da Turkiyya sun sanar da rattaba hannu kan yarjeniyoyi da dama a ziyarar farko cikin shekaru 10 da shugaban kasar Turkiyya Recep Tayyip Erdogan ya kai wa wannan masarauta a yankin tekun Fasha.

Kamfanin dillancin labarai na Ahlul-Baiti {a.s} - ABNA - Wannan dai ya tabbatar da kusanci tsakanin tsoffin abokan hamayyan biyu.

Shugaban kasar Recep Tayyip Erdoğan ya gana da yarima mai jiran gado na UAE Sheikh Mohammed bin Zayed Al Nahyan a ziyarar da ya kai birnin Abu Dhabi.

A yayin ganawar, an tattauna hadin gwiwar dake tsakanin kasashen biyu da kuma ci gaban yankin.

Bin Zayed ya yi fatan wannan muhimmiyar ziyara za ta zama mafarin gina wani sabon lokaci wajen karfafa hadin gwiwa tsakanin kasashen biyu..

Ya bayyana cewa, za su yi maraba da dukkan matakan da aka dauka na samar da zaman lafiya da hadin gwiwa a shiyyar, kuma kasarsa na mai da hankali kan hadin gwiwa da kasar Turkiyya.

342/