Kamfanin Dillancin Labarai Na AhlulBaiti

Madogara : Hausatv
Talata

15 Faburairu 2022

16:37:05
1229885

Mali: Faransa Za Ta Janye Sojojinta Daga Kasar Amma Zata Wanzar Da Su A Sahel

Ministan harkokin wajen kasar Faransa Jean-Yves Ledrian ya bayyana cewa gwamnatin kasar Faransa zata janye sojojinta daga kasar Mali, amma za ta ci gaba da wanzar da samuwar sojojinta a sauran kasashen yankin Sahel.

Kamfanin dillancin labarai na Ahlul-Baiti {a.s} - ABNA -nakalto Le-Darain yana fadar haka bayan taron tattaunawa tsakanin kasashen da suke da sojojinsu a kasar Mali da kuma wasu manya manyan kasashen yamma a jiya Litinin ta hotunan bidiyo.

Ministan ya ce babu bukatar faaransa ta ci gaba da ajiye sojojinta a kasar Mali, don babu fahintar juna da gwamnatin sojojin da suke iko da kasar a halin yanzu.

Labarin ya kara da cewa a gobe Laraba ce ake saran shuwagabannin ragowar kasashen Sahel 3 wato Niger, Chadi da Mauritani zasu gudanar da taro kan matsalar ta Mali. Har’ila yau an gayyaci Najeriyacikin a taron na gobe. Amma banda Mali da Burkina Faso.

342/