Kamfanin Dillancin Labarai Na AhlulBaiti

Madogara : Hausatv
Talata

15 Faburairu 2022

16:19:09
1229877

Shugaban Ukraine Ya Ayyana Laraba A Matsayin Ranar Hadin Kai

Shugaban Ukraine Ya Ayyana Ranar Laraba, wacce ake hasashen rasha za ta farmawa Kasar, a Matsayin Ranar Hadin Kai.

Kamfanin dillancin labarai na Ahlul-Baiti {a.s} - ABNA -A cikin wani jawabi ga al'ummar kasar jiya Litini, Volodymyr Zelensky ya ayyana ranar Laraba a matsayin ranar hadin kai, wanda kafafen yada labarai suka ambato a matsayin ranar da Rasha za ta iya kai wa kasar hari.

Ya kira al'ummar Ukraine a ranar da su rataye tutar kasar tare da nuna launin shudi da rawaya na kasar.

A halin da ake ciki dai Sakatare Janar na MDD Antonio Guterres ya yi kira da a yi amfani da diflomasiyya wajen yayyafawa rikicin Rasha da Ukraine ruwa sanyi.

Antonio Guterres, ya ce ya damu ainun da dumammar yanayi da karuwar cece-kuce game da yuwuwar aukuwar yaki.

Ya ce jefa bil adama cikin damuwa da wargaza tsaron nahiyar Turai da ma duniya baki daya, abu ne mai matukar tsanani, don haka ba za su amince da irin wannan fito na fito mai hadari ba.

Da farko a jiyan, Sakatare Janar din ya tatatuna ta kafar bidiyo da ministan harkokin wajen Rasha Sergei Lavrov. Ya kuma yi wata tattaunawar ta daban, da ministan harkokin wajen Ukraine Dmytro Kuleba.

342/