Kamfanin Dillancin Labarai Na AhlulBaiti

Madogara : Hausatv
Talata

15 Faburairu 2022

16:18:29
1229876

Le Drian : Faransa Za Ta Ci Gaba Da Yaki Da Ta’addanci A Sahel, Amma Ba A Mali Ba

Ministan harkokin wajen Faransa, Jean-Yves Le Drian, ya ce kasar za ta ci gaba da yaki da ta’addanci a yankin Sahel amma ba a kasar Mali ba.

Kamfanin dillancin labarai na Ahlul-Baiti {a.s} - ABNA -Ya ce idan yanayin da ake bukata na kasancewa a Mali, bai samu ba, to zasu ci gaba da yaki da ta’addanci a kusa, tare da sauren kasashen yankin sahel wadanda suka bukaci hakan.

Kalamman na Mista Le Drian, na zuwa ne ‘yan sa’’o’I bayan wani taron kafar bidiyo na ministocin harkokin wajen kasashen turai a jajibirin wata ganawa da shugaba Emanuel Macron zai yi da takwarorinsa uku na yankin sahel da suka hada da na Nijar, Chadi da kuma Mauritania.

Faransa dai na cewa ba ta ga ta zama a Mali ba, duba da zuwan sojojin dake son dawwama kan mulki da kuma kasancewar sojojin haya na Rasha na Wagner, da Jean-Yves Le Drian din, ya kiyasta cewa zasu kai 1,000 a yanzu a kasar ta Mali.

342/