Kamfanin Dillancin Labarai Na AhlulBaiti

Madogara : Hausatv
Asabar

12 Faburairu 2022

16:22:07
1228853

EU Za Ta Zuba Jarin Sama Da Yuro Biliyan 150 A Afrika

Kungiyar tarayyar Turai EU ta sanar da aniyarta ta zuba jarin Euro sama da biliyan 150 a Afrika nan da wasu shekaru masu zuwa a matsayin wani bangare na aniyar farko na shirin zuba jari mai suna Global Gateway, kamar yadda shugabar hukumar gudanarwar EU, Ursula von der Leyen, ta sanar a Dakar, babban birnin kasar Senegal.

Kamfanin dillancin labarai na Ahlul-Baiti {a.s} - ABNA -Von der Leyen, ta yi wannan tsokaci ne a taron manema labarai na hadin gwiwa tare da shugaban kasar Senegal Macky Sall, sai dai ba ta yi wani karin haske game da batun shirin zuba jarin ba.

A cewarta, za a gudanar da taron dandalin hadin gwiwar EU da Afrika a ranakun 17 zuwa 18 ga watan nan na Fabrairu a birnin Brussels, wanda shi ne kashin farko na shirin hadin gwiwar bunkasa tattalin arziki tsakanin bangarorin biyu, wanda zai gudana karkashin sabon shirin bunkasa zuba jari a fannin gina kayayyakin more rayuwa na Global Gateway.

Von der Layen ta ce, tabbas suna bukatar bangarorin masu zaman kansu, da kwararru da kuma jari mai karfi, kuma suna bukatar tsarin shugabanci a matakin koli.

342/