Kamfanin Dillancin Labarai Na AhlulBaiti

Madogara : Hausatv
Jummaʼa

11 Faburairu 2022

12:52:57
1228393

Borrell : An Zo Gabar Karshe A Tattaunawar Vienna

Shugaban kula da harkokin kasashen turai, Josep Borrell, ya bayyana cewa an zo wata gaba ta karshe game da tattaunawar da ake a Vienna da nufin farfado da yarjejeniyar nukiliyar Iran.

A ranar Talata da ta gabata ce aka koma zagaye na takwas na tattaunawar da ake game da yarjejeniyar nukilioyar ta Iran, bayan dakatarwa na dan lokaci.

Jami’in ya kuma yi fatan tattaunawar za ta haifar da da mai ido cikin kankanin lokaci, duk da a cewarsa har yanzu akwai ‘yan sabanin dake akwai.

Dukkanin bangarorin a cewarsa sun nuna kyakyawar niyya.

A ranar farko ta tattaunawar jami’I mai wakiltar kasar Sin, ya bayyana cewa sun dukufa wajen cimma matsaya ta karshe.

342/