Kamfanin Dillancin Labarai Na AhlulBaiti

Madogara : Hausatv
Lahadi

6 Faburairu 2022

18:55:31
1226719

​Kasar Rasha Ta yi Maraba da Matakin Da Amurka Ta Dauka Na Cirewa Iran takunkumi

Wakilin kasar rasha a tattaunawar da ake yi a birnin Vienna na cirewa iran takunkumi Mikha’il Ulyanov ya fadi cewa mataki cire wa Iran takunkumi da Amurka ta dauka yana kan sahihiyar hanya kuma zai taimaka wajen gaggauta kulla yarjejeniya a tattaunawar da ke yi da kuma dawowar Amurka cikin tattaunawar , kuma ya nuna alamun cewa an shiga matakin karshe a tattaunawar

Kamfanin dillancin labarai na Ahlul-Baiti {a.s} - ABNA - Kasar Amurka ta sanar da dage takunkumi kan shirin nukiliyar Iran na zaman lafiya, a matsayin wani mataki na nuna aniyarta ta dawowa cikin tattaunawar da aka kulla yarjejeniya a kai a shekara ta 2015.

Anasa bangaren kakakin ma’aikatar harkokin wajen kasar Iran Saed Khatib Zade ya fadi cewa iran dama tana jiran Amurka ta cika alkawuran da ta dauka da kuma aiki da nauyin da ya rataya a wuyarta na cirewa iran takunkumi , yace abin da ya fi dacewa shi ne Amurka ta cire dukkan takunkumin da ta kakabawa kasar Iran,

342/