Kamfanin dillancin labarai na Ahlul-Baiti {a.s} - ABNA - Associated Press ta bayyana cewa gwamnatin Biden ta yi haka ne don ganin an gaggauta kammala tattaunawa da take gudana a halin yanzu a birnin Vienna na kasar Astria na dagewa Iran dukkan takunkuman da Amurka ta dora mata bayan ficewar ta daga yarjejeniyar kimani shekaru 4 da suka gabata.
Gwamnatin Biden dai ta ce tana son dawowa cin yarjejeniyar amma tana jan kafa wajen dawowar saboda tana son samun lamuni daga Iran kan wasu al-amura. Sai dai gwamnatin Iran ta dage kan dole ne Amurka ta dage dukkan takunkuman da aka dora mata tun bayan ficewarta daga yarjejeniyar.
342/