Kamfanin Dillancin Labarai Na AhlulBaiti

Madogara : Hausatv
Lahadi

30 Janairu 2022

17:05:40
1224286

​Mali: Faransa Ta Ce Ba Za Ta Ci Gaba Da Ajiye Sojojin A Kasar Idan Hakan Da Tsada Ba

Ministan tsaron kasar Faransa Florence Parly ta bayyana cewa kasashen turai zasu ci gaba da kula da sojojinsu da suke tabbatar da zaman lafiya a kasar Mali, amma akwai iyakan kudaden da kasar Faransa zata kashe saboda hakan.

Kamfanin dillancin labarai na Ahlul-Baiti {a.s} - ABNA - bayyana cewa dangantaka tsakanin gwamnatin sojoji na kasar Mali da kasashen Turai sun kusan katsewa saboda rashin gudanar da zabe a kasar a farkon wannan shekara ta 2022 bayan juyin mulki har sau 2 wanda sojojin kasar suka yi a bara.

A ranar laraban da ta gabata ce gwamnatin sojojin kasar ta Mali ta bukaci kasar Faransa ta daine shiga cikin harkokin cikin gida na kasarta. Daga karshe Paly ta ce:

'ci gaba da kasancewar sojojin kasar Faransa a Mali yana kara tsada, sannan dole ne gwamnatin kasar ta kaiyade abinda zata kashe don kula da sojojinta a kasar Mali'.

Kasar Mali dai tana fama da 'yan bindiga wadanda suke riya addini a arewacin kasar da kuma wasu kasashe makobta da kasar. Wadanda

342/