Kamfanin Dillancin Labarai Na AhlulBaiti

Madogara : Hausatv
Lahadi

30 Janairu 2022

17:01:22
1224283

​Moscow: Yadda Kafafen Yada Labaran Turai Ke Kanbama Batun Ukraine Ya Kai Kololuwar Hauka

Ma'aikatar harkokin wajen Rasha ta yi tsokaci kan wani rahoton da kafafen yada labarai na yammacin Turai suka fitar, inda suka zargi Rasha da tura "manyan dakaru" zuwa kan iyakar kasar da Ukraine, bayanin ya ce; bisala'akari da yadda kafafen yada labaran yammacin duniya ke yada jita-jita game da Ukraine ya kai ga mataki nahauka.

Kamfanin dillancin labarai na Ahlul-Baiti {a.s} - ABNA - Ta kara da cewa duk wata kafar yada labarai da ke bayar da labarai na karya dangane da hakan, ta zubar da kimarta ta kafar sadarwa, amma gidan rediyon SRF na kasar Switzerland ya zarta kowa ta hanyar fitar da wani faifan bidiyo mai taken: "Rasha na tura dakarunta zuwa kan iyakar kasar da Ukraine."

Ma’aikatar harkokin wajen Rasha ta ce, tura sojoji zuwa Belarus da ta yi, yana da alaka ne da wani shirin atisayi, wanda kuma wannan ba sabon lamari ba ne, an kwashe tsawon shekaru ana yin irin haka tsakanin Rasha da Belarus.

Bayanin ya ce daga ranar 10 zuwa 20 ga watan Fabrairu, za a gudanar da atisayen hadin gwiwa tsakanin sojojin Rasha da Belarus a cikin kasar ta Belarus, inda dakarun za su kara samun horo kan kare kashensu daga duk aikin wuce gona da iri daga wata kasa, da kuam yaki da ‘yan ta’adda.

Ko a ranar Juma’ar da ta gabata dai shugaban Ukraine ya bayyana cewa, kasashen turai suan kanbama batun kasar tasa, tare da jefa tsoro a cikin zukatan al’ummar kasar, alhali babu wata barazana ta a zo a gani a halin yanzu da kasar ke fuskanta daga Rasha.

342/