Kamfanin Dillancin Labarai Na AhlulBaiti

Madogara : Hausatv
Asabar

29 Janairu 2022

20:03:16
1223900

Kungiyar EU Ta yi Kira Da A Sanya Siyasa Wajen Yanke Shawara A Tattaunawar Vienna

Mai shiga tsakanin na kungiyar tarayyar turai kan tattaunawar da ake yi na cirewa Iran takunkumi a birnin Vieanna na kasar Austeriya zagaye na 8 tsakanin iran da kasashen jamus faransa birtaniya rasha china da , ya bukaci a yi amfani da siyasa wajen yanke shawara kan yarjejeniyar ada ake cimma a tsakani,

Kamfanin dillancin labarai na Ahlul-Baiti {a.s} - ABNA - Wannan yana zuwa ne bayan da aka tsayar da tattaunawar na tsawon makon guda domin bada dama ga wakilan mahalarta taron sun koma kasashen su domin yin shawarwarwaye kan abubuwa da aka tattaunawa kafin cimma matsaya akai,

Batun cirewa Iran takunkumi ba tare da wani sharadi ba, da kuma bada tabbacin cewa iran ba za ta fice daga yarjejeniyar ba, suna daga cikin manyan ginshikan tattaunawar da iran ta dage akai.

342/