Kamfanin Dillancin Labarai Na AhlulBaiti

Madogara : Hausatv
Asabar

29 Janairu 2022

19:57:41
1223892

​Amurka Ta Bukaci “ Yan Kasarta Su Fice Daga UEA Saboda Barazanar Tsaro Daga Yemen

Ma’aikatar harkokin wajen Amruka ta fitar da sanarwa ta gargadi ga ‘yan kasar da su nesanci zuwa UEA, da babban birninta Abu Dhabi, saboda barazarar hare-haren makamai masu linzami da jiragen sama marasa matuki daga Yemen.

Kamfanin dillancin labarai na Ahlul-Baiti {a.s} - ABNA - Sanarwar ta cigaba da cewa da akwai baraza babba akan yiyuwar hare-haren su cutar da Amurkawa da kuma manufofinsu da ke kasar, musamman bayan sanarwar da ta fito daga Yamen na kai wa UEA hari.

A farkon wannan makon mai karewa ne dai gwamnatin kasar Yemen mai babban birni a San’aa ta yi kira ga ‘yan kasashen waje mazauna UEA da su fice daga cikinta,domin daga yanzu kasar ba ta da aminci.

Shekaru 7 kenan a jere da Saudiyya da UEA suka shelanta yaki akan kasar Yemen, wanda ya zuwa yanzu ya ci dubban rayuka.

Sojojin kasar ta Yemen dai sun kai hari da jiragen sama marasa matuki akan wasu cibiyoyi 3 na UEA a babban birnin kasar Abu Dhabi, wanda ya haddas asarar rayuka da dukiya.

342/