Kamfanin Dillancin Labarai Na AhlulBaiti

Madogara : Hausatv
Alhamis

27 Janairu 2022

18:28:01
1223248

​Dan Takarar Shugabancin Faransa Eric Zemour Ya Ce Takaita Harkokin Musulunci Idan ya Ci Zabe

Eric Zemour dan takarar shugaban kasar Faransa mai ra'ayin rikau, ya bayyana shirinsa na sanya takunkumi kan Musulunci da alamomin Musulmi idan ya yi nasara.

Kamfanin dillancin labarai na Ahlul-Baiti {a.s} - ABNA - Tashar aljazeera ta bayar da rahoton cewa, Zemour ya wallafa bayanin ne a shafinsa na Twitter, inda ya bayyana cewa: Za a haramta sanya duk wani tufafi da ke dauke da alamomin Musulunci - ciki har da hijabi a wuraren da jama'a ke taruwa.

Bugu da kari, ya yi alkawarin haramta ayyukan kungiyoyin Musulunci, kamar kungiyar 'yan uwa musulmi, idan ya yi nasara.

A baya Zemour ya bayyana a wata hira da tashar talabijin ta France 2 cewa: "Idan ya zama shugaban kasa, zai hana Musulman Faransa sakawa 'ya'yansu sunan Muhammad."

Ya jaddada a cikin hirar cewa dokar za ta sanya kaidi kan sunayen da ake radawa yaran musulmi.

Wasu masu fafutuka musulmi sun jaddada cewa idan Eric Zemour ya lashe zaben shugaban kasa, da dama daga cikin al'ummar musulmi da Larabawa a Faransa za su fice daga kasar.

342/