Kamfanin Dillancin Labarai Na AhlulBaiti

Madogara : Hausatv
Laraba

26 Janairu 2022

17:17:50
1222822

Mahalarta Taron Tattaunawa Kan Cirewa Iran Takunkumi A Veinna Sun Gana Da Tawagar Amurka

Babban mai shaiga tsakani na kasar Rasha a tattaunawar da ake yi ta cirewa iran takunkumi a birnin Vienea Mikail Ulyanov ya wallafa a shafinsa na twitter cewa mahalarta taron na JCPOA sun gana da wakilan Amurka ba tare da kasar Iran ba, domin duba ci gaban da aka samu a tattaunawar.

Kamfanin dillancin labarai na Ahlul-Baiti {a.s} - ABNA - Mafiyawancin mahalarta taron zagaye na 8 da aka fara a ranar 27 ga watan Decemba day a gabata sun yi ammanna cewa an samu ci gaba sosai a tattaunawar ta neman cirewa iran takunkumi

An gudanar da ganawar tsakanin wakilain kasashen turai biyar da na Amurka ne a otel din Marriott dake gaban wajen da ake tattaunawa kan batun cirewa iran takunkumi

Batun hanyoyin da za’a bi wajen cirewa Iran ta kunkumi da kuma bada lamuni na daga cikin muhimman batutuwa biyu da iran ta dage a akai a tattaunawat ta Vieanna.

342/