Kamfanin Dillancin Labarai Na AhlulBaiti

Madogara : Hausatv
Lahadi

23 Janairu 2022

14:06:05
1221711

Burtaniya: Wata ‘Yarmajalisa Ta Ce An Tubeta A Matsayin Minista Ne Don Ita Musulma Ce

Wata ‘yar majalisar a majalisar dokokin kasar Burtaniya Nusrat Ghani ta bayyana cewa jam’iyyarta ta ‘Conservative’ karkashin gwamnatin Boris Jonson ta tubeta daga kan kujerar ministan sifiri ne don ita musulma ce.

Kamfanin dillancin labarai na Ahlul-Baiti {a.s} - ABNA - Tashar talabijin ta Presstv a nan Tehran ta kakalto Nusrat Ghani diyar shekara 49 a duniya tana fadawa wasu kafafen yana labarai kan cewa, dogarin m,ajalisar ko wip ne ya bata labaran dalilin tube ta, ya ce a wata zama a fadar dawning street ne wasu ‘yan jam’iyyarta suka tado batun musuluncinta, wanda ya kai ga tube ta a kan kujerrar minister sifiri.

Nusrat dai ita ce musulma ta farko wacce ta taba rike kujerar minista a gwamnatin kasar Burtaniya. Daga karshe Nusrat ta kammala da cewa a halin yanzu ta rasa yardar da takewa jam’iyyarta ta Conservative, kuma mai yuwa ta dauki wasu matakai nan gaba.

342/