Kamfanin Dillancin Labarai Na AhlulBaiti

Madogara : Hausatv
Lahadi

23 Janairu 2022

13:59:57
1221703

​Tarayyar Turai: Rusa Gidajen Falasdinawa Ya Saba Wa Doka

Kungiyar Tarayyar Turai EU ta bayyana cewa tsugunar da yahudawa a yankunan da Isra'ila ta mamaye da kuma rusa gidajen Falasdinawa haramun ne a karkashin dokokin kasa da kasa,

Kamfanin dillancin labarai na Ahlul-Baiti {a.s} - ABNA - A wata sanarwa da kakakin kungiyar Tarayyar Turai EU ya fitar, ya ce rushe gidajen Falasdinawa biyu da ke unguwar Sheikh Jarrah wani lamari ne mai hatsarin gaske wanda yake kara ta'azzara tarzoma.

Ya kuma yi kira ga gwamnatin Israila da ta sake duba shirinta na gina gidaje 1,450 a garuruwan Har Hawma da Gafat Hamutos, tare da dakatar da duk wasu gine-gine a yankunan Falasdinawa da ta mamaye.

Kungiyar Tarayyar Turai ta bayyana shirinta na taimakawa wajen samar da damar sake farfado da tattaunawar sulhu tsakanin Falasdinu da Isra'ila.

Wannan dai na zuwa ne a daidai lokacin da gwamnatin Isra'ila take ci gaba da tafka laifuka a kan al'ummar Falasdinawa, da kuma tilasta musu barin gidajensu na yankunansu domin tsugunnar da yahudawa yan share wuri zauna.

Dangane da haka; Yahudawan sahyuniya sun tilasta wa wani bafalastine rusa gidansa a karo na biyu sannan wani sun tilasta shi ya rusa shagonsa da ke sansanin Shafat a arewacin birnin Kudus da aka mamaye.

342/