Kamfanin Dillancin Labarai Na AhlulBaiti

Madogara : Hausatv
Jummaʼa

21 Janairu 2022

21:42:12
1221111

Za’a Gudanar Da Atisayin Hadin Gwiwa Tsakanin Iran, Rash Da Chaina A Tekun Indiya

Rahotanni sun bayyana cewa A ranar juma’ar nan ce ake sa ran kasar Iran za ta gudanar da atisayi na sojojin ruwa a Arewacin tekun indiya da zai samu halartar kasashen Rasha da China, kuma tuni jiragen ruwan kasar iran suka yi maraba da jiragen ruwan kasashen biyu

Kamfanin dillancin labarai na Ahlul-Baiti {a.s} - ABNA - Har ila yau rahoton ya ci gaba da cewa bayan kwaryakwaryan biki da aka gudanar bayan isa jiragen ruwan kasashen rasha da china an gudanar da taron tsakanin bangarorin game da yadda atisayin zai kasance

Kakakin runudanar shirya Atisayin Real Admiral Mostafa Taj Al’din ya fadi cewa atiyasan soojin ruwa na hadin guiwa da tsaron ruwa na shkarata ta 2022 za’a gudanar da shi ne karkashin taken aiki tare don tabbatar da zaman lafiya da tsaro a yanki mai fadin murabba’in kilo mita 17000

Ya kara da cewa babbar manufar yin Astiyan shi ne karfafa tsron yankin da na kasuwancin teku da kuma yaki da satar fasaha da ta’adanci a cikin teku da kuma mausayar bayanan sirri

342/